Hukumar CAC za ta fara farautar masu sana’ar POS da basu yi rajista da ita ba
Hukumar Rajistar Kamfanoni (CAC) ta bayyana cewa za ta fara cafke dukkan masu gudanar da ayyukan na’urar biyan kuɗi (POS) da ba su yi rajista ba daga ranar 1 ga Janairu, 2026.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta bayyana yawaitar na’urorin POS da ba su yi rajista ba a matsayin “aiki babu ka’ida” wanda ya saba wa dokokin Companies and Allied Matters Act (CAMA) na 2020 da kuma ka’idar aikin dillalan banki ta Babban Bankin Najeriya (CBN).
KU KUMA KARANTA: Nafisa ta cancaci shugaba Tinubu ya yi mata kyautar dala dubu 100, gida da OON — Pantami
“Wannan aiki marar ka’ida, wanda wasu kamfanonin fasaha na kuɗi ke taimakawa, na iya jefa tsarin kuɗin Najeriya da dukiyar jama’a cikin haɗari. Wannan dole ne ya tsaya,” in ji CAC.
Sanarwar ta ƙara da cewa babu wani mai gudanar da POS da za a bari ya yi aiki ba tare da rajista a CAC ba, kuma hukumomin tsaro za su tabbatar da bin wannan umarni a faɗin ƙasar.









