Tsaro: Gwamnan Kano ya ziyarci sansanin JTF a Tsanyawa da Shanono

0
78
Tsaro: Gwamnan Kano ya ziyarci sansanin JTF a Tsanyawa da Shanono

Tsaro: Gwamnan Kano ya ziyarci sansanin JTF a Tsanyawa da Shanono

Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya ziyarci sansanin rundunar haɗin gwiwa ta JTF a Karamar Hukumar Tsanyawa, inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro wajen magance barazanar tsaro da ta taso a yankin.

Gwamnan ya ce ziyarar tasa ta nufin tantance halin tsaro da ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro, yana mai bayyana cewa ayyukan JTF za su dawo da zaman lafiya a yankunan da suka gamu da hare-hare.

KU KUMA KARANTA: Taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas: Dole ne mu ƙarfafa haɗin kai don dakatar da matsalar tsaro – Gwamna Buni

Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ba da dukkan goyon baya, musamman a fannin jin daɗin jami’an tsaro da samar da kayan aiki, tare da tabbatar da cewa waɗanda aka sace za a kubutar da su cikin koshin lafiya.

Shugaban rundunar ta 3 na Sojan Najeriya, Birgediya Janar Ahmed Tukur, ya bayyana cewa rundunar ta ƙunshi jami’an soji, rundunar sojan sama, ‘yansanda, DSS, NSCDC da ‘yan sa-kai, kuma suna gudanar da ayyuka a wuraren da ake fama da barazana.

Gwamnan ya kuma ziyarci kauyen Yankamaye, inda aka sace mutane shida tare da kashe wata tsohuwa.

Leave a Reply