No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sojoji sun ceto mutune 7 da aka yi garkuwa da su a Kano

Sojojin Operation MESA da suka haɗa da jami’an Birgediya ta 3 ta rundunar sojin Najeriya, sojojin saman Najeriya da kuma ’yansanda sun ceto mutune bakwai da aka yi garkuwa da su yayin wani samame da suka kai da daddare a karamar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron sun samu kiran gaggawa misalin ƙarfe 11 na dare a ranar 29 ga Nuwamba 2025 kan harin ’yan bindiga a kauyen Yankamaye Cikin Gari. Sojojin da suka garzaya cikin gaggawa sun shiga musayar wuta da ’yan bindigar, waɗanda kafin isowarsu suka riga suka kashe wata mata ’yar kimanin shekara 60.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe wani da su ka yi garkuwa da shi, saboda rashin isasshen kuɗi a asusunsa na Banki

Bayan yin hargitsi da ’yan bindigar, sojojin sun bi sawun su zuwa hanyar Rimaye, inda suka ci gaba da musayar wuta kuma suka ƙwato waɗanda aka yi garkuwa da su. Sai dai mutane huɗu daga cikin waɗanda aka sace har yanzu ba a gan su ba.

Rahotoanni sun bayyana cewa ’yanbindigar sun tsere zuwa karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina, kuma ana ci gaba da kokarin gano inda suke.

Kwamandan Birgediya ta 3 ya yabawa sojojin bisa jarumta da gaggawar da suka nuna, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar samar da sahihan bayanai cikin lokaci.

Sanarwar ta fito ne daga Babatunde Zubairu, Kyaftin kuma Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar soji, Birgediya ta 3.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...