Shaikh Zakzaky ya miƙa saƙon ta’aziyya bisa ga rasuwar Shaikh Ɗahiru Bauchi

0
176
Shaikh Zakzaky ya miƙa saƙon ta'aziyya bisa ga rasuwar Shaikh Ɗahiru Bauchi

Shaikh Zakzaky ya miƙa saƙon ta’aziyya bisa ga rasuwar Shaikh Ɗahiru Bauchi

Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa bisa rasuwar fitaccen Malamin addinin Musulunci, Shaikh Dahiru Usman Bauchi.

A cikin saƙon ta’aziyyarsa wadda ofishin Shehin Malamin ya fitar a yau Alhamis, Jagoran Harkar Musuluncin, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ya bayyana rasuwar malamin a matsayin “babban rashi mai nauyi, wanda ya shafi al’umma baki ɗaya.” Ya miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin, ɗalibansa, da ɗaukacin masoyansa, tare da roƙon Allah madaukaki Ya jiƙan marigayin, Ya yafe masa, kuma Ya azurta shi da Aljannah.

Shaikh Zakzaky ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba wa iyalai, dangi, da masoya haƙuri da juriyar wannan babban rashi.

KU KUMA KARANTA: Fitaccen Malamin addini Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya

Al’ummar musulmi a Nijeriya da ma ƙasashen duniya sun shiga cikin wani mawuyacin lokaci na jimami bayan labarin rasuwar fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Usman Ɗahiru Bauchi (Rahimahullah), wadda ta faru a safiyar yau Alhamis, 06/Jumada al-Thani/1447H, daidai da 27/11/2025.

KU KUMA KARANTA: Fitaccen Malamin addinin musulunci, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya rasu

Sheikh Usman Ɗahiru Bauchi ya kasance shahararren malami mai zurfin ilimi da basira, wanda dubban ɗalibai da malamai suka amfana da gagarumar gudummawarsa wajen yaɗa ilimi, inganta tarbiyya, da karfafa amana cikin al’umma. Rashinsa ya bar babban giɓi da kule ga al’ummar Musulmi, musamman ma waɗanda suka tashi a ƙarƙashin karantarwarsa.

A halin yanzu, masoya na ci gaba da gudanar da addu’o’i, musamman karatun Suratul Fatiha, domin neman rahamar Ubangiji ga malamin da ya yi babban tasiri ga rayuwar mutane da dama.

Leave a Reply