Chelsea ta lallasa Barcelona da ci 3-0 a wasan zakarun Turai
A ci gaba da zagayen wasan zakarun Turai, a ranar Talata aka buga wasa tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta Ingila da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta Spain.
Wasan ya ba da mamaki matuƙa, ganin yadda Chelsea ɗin ta lallasa Barcelona da ci 3-0.
KU KUMA KARANTA: Real Madrid, Manchester United, Chelsea da Liverpool sun sha kashi a gasar Firimiya da Laliga
Kounde ne ya ci gida a minti 27. Sai kuma Estevao ya ƙara zura ƙwallo ta biyu a minti 55. Inda Delap ya zura ƙwallo ta uku a minti 73.

Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Barcelona Ronald Araujo, ya samu jan kati, sakamakon doke Cucurela.










