Damina Uwar Albarka 

0
235
Damina Uwar Albarka 
Yusuf Alhaji Lawan

Damina Uwar Albarka

Daga Yusuf Alhaji Lawan

A ƙarshen rani, daga bazara zuwa gaba, lokaci ne da ciyayi ke bushewa, ƙoramu ke ƙafewa, to irin wannan lokacin ya fi tsanani ga makiyaya, musamman ma na daji. Riƙe dabbobi na ba su wahala ƙwarai da gaske. A lokacin ne kuma ake fara samun hauhawar farashin kayan abinci.

Bayan nan kaɗan ne manoma ke ƙoƙarin fara shirye-shiryen aikin gona. Manoma da yawa na farawa ne da sassabe a gona, yayin da wasu ke ƙona ciyayi da suka bushe da kuma tattara duk wani dangin tsiro da ba’a buƙata a gonar, aikin da wasu ke ƙira da sharar gona. Kai wa taki gona kan zama mataki na gaba. Takin da ake kai wa a lokacin shi ne takin gida, wato na gargajiya. Kuma daga nan sauran shirye-shirye ke fara kankama.

Bayan an yi ruwan farko ko na biyu a wasu wurare, bisa la’akari da abin da mutum zai noma idan ya danganci kayan tsaba ne, akan nemi masu shanu, su je gonar da garma su yi huɗa. Yawanci, ladan su yana danganta ne da adadin kunya da suka yi. A wasu wurare akan ƙirga kunya nawa suka yi, sai a biya su ko kuma ayi jingar aikin duka tun kafin a fara, sai a daidaita, idan sun gama sai a biya.

Daga nan sai kuma lokacin da manomi ya gamsu da yawan ruwan sama da aka yi, ya kai ya yi shuka, sai ya ɗauki iri da sauran kayan aiki kamar su sungumi da fartanya da kwacciya (ƙaramar ƙwarya ce da ake zuba iri ana shuka da ita) ya nufi gona domin yin shuka. Bayan shuka da wani ɗan lokaci, ciyawa kan tsiro ta ko ina a cikin gona, har ta kan rufe shukar ma. To idan haka ta faru, akan yi noma domin a cire ciyayin da suka tsiro don a bawa shukar damar numfasawa yadda ya kamata. Maimakon nome ciyayin, wasu kan yi amfani da maganin kashe ciyayi, sai su fesa a gonar domin ciyayin su mutu.

In an shuka gero ko masara ko dawa da sauran su, bayan sun tsiro, wasu na buƙatar rage, saboda sama da uku sun tsiro, sai ayi musu. Rage shi ne tugewa ko cirewa na kaɗan daga tsiron shuka. To bayan an yi rage, a lokuta mafiya yawa, mataki na gaba shi ne saka takin zamani a gonar da ke buƙatar hakan. Shi kuma takin zamani ana saka shi ne a wani tsari da ake ce masa ga-naka. Wannan tsari ne na zuba takin a gefen kowace tsiron shuka bayan ta fito. Wasu na kiran sa da kai-ga-naka ne saboda kowane tsiron shuka sai an sa masa. Abu na gaba shi ne saka maganin ƙwari. Wannan na da muhimmanci sosai ga yankin da ke fama da matsalar ƙwari da ke lalata amfanin gona. Bayan an gama duk waɗannan da wani ɗan lokaci, sai tsirran su girma har su fitar da kai.

KU KUMA KARANTA: Jihohin Kogi, Anambara da Yobe za su fuskanci mummunar ambaliyar ruwa a daminar bana – NiMet

Kamar gero, idan ya nuna, akan yanka ayi tumu, wato a gasa shi a ci yadda ake cin gasasshiyar masara. Sai dai banbancin shi ne, shi tumu ba’a cin sa kai tsaye daga jikin zangarniyar sa, sai dai a zage akan faifayi ko makamancin sa musamman ana gama gasawa tun yana da zafin sa, sai a tsince, a ci. Ana kiyaye cin ɓuntu saboda ana cewa yana maƙalewa a maƙogoro yaƙi wucewa, hakan kuma na wahalarwa sosai.

Alamar wake zai yi kyau shi ne a ga yana yaɗo da furanni. Gyaɗa kuma ta tsiro da ganye sai gero da masara da dawa da sauran su kuma su fidda kai. Bayan amfanin gona ya gama nuna, abu na gaba shi ne girbi. A lokacin girbi, ana zuwa da magirbi, sai a girbe irin su gero da dawa da sauran su. Bayan anyi girbi, wato an kwantar da karan tare da amfanin a jikin sa, sai ayi amfani da wuƙa a yanke amfanin, wato a raba amfanin da karan da ya goya shi. Bayan an gama yanka, sai a tara amfanin, a ɗaure su da igiya, ayi su dami-dami, sai a kwashe a kai rumbu.

Idan buƙata ta taso, sai a je rumbu, a ɗauko amfanin adadin yadda ake so, sai ayi sussuka, a sheƙe, a reraye, a bakace, a zuba a buhu, ayi amfani da musulla da kirtani a ɗinke buhun. Masara kuwa karye ta ake yi. Sannan akwai fyaɗar gyada, roron wake da cin borkono. Bayan an gama duka waɗannan, aka kwashe tsaba aka killace, to kuma akan samu ƙaiƙayi, kowar wake da harawar gyada da karmamin dawa da karan gero da sauran su. Su kuma waɗannan abincin dabbobi ne, kuma za’a iya ganin su a matsayin ribar ƙafa.

Kamar haka tsarin aikin noma yake musamman ga kayan tsaba, wanda ake yi daga gabanin damina zuwa ƙarshen ta. “Noma tushen arziƙi, na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya, kai ya tarar”.

Yusuf Alhaji Lawan ya rubuta daga anguwar Hausawa Asibiti, garin Potiskum jihar Yobe. Za’a iya tuntuɓar sa ta nasidi30@gmail.com.

Leave a Reply