Ɗan wasan Chelsea, Palmer ya karya babban ɗan yatsan ƙafar sa sakamakon tuntuɓe da ƙofa

0
131
Ɗan wasan Chelsea, Palmer ya karya babban ɗan yatsan ƙafar sa sakamakon tuntuɓe da ƙofa
Ɗan wasan gaba na Chelsea

Ɗan wasan Chelsea, Palmer ya karya babban ɗan yatsan ƙafar sa sakamakon tuntuɓe da ƙofa

Ɗan wasan gaban Chelsea, Cole Palmer zai ƙara yin jinya ta a kalla mako guda saboda ya karye a babban ɗan yatsar ƙafarsa lokacin da ya buge da ƙofar daki a ranar Laraba.

Dan wasan gaban Chelsea da Ingila na daf da komawa atisaye a wannan makon bayan ya shafe watanni biyu yana jinya ciwon cirar nama da ya samu.

Sai dai dan shekara 23 ɗin zai cigaba da zama na ɗan ƙarin lokaci saboda raunin da ya samu a babban yatsan ƙafarsa ta hagu.

KU KUMA KARANTA: An dakatar da ɗan wasan Chelsea daga ƙwallo

Ba zai samu buga wasannin uku na gaba ba da suka haɗa da Firimiya, tsakanin Chelsea da Burnley a yau Asabar sai kuma wasan zakarun nahiyar turai na ranar Talata da Barcelona, da kuma wasan mako mai zuwa da Arsenal a Stamford Bridge.

“Tabbas ba zai buga wasan Asabar ba, haka nan ba na Barcelona ba, ko Arsenal,” in ji kocin Chelsea, Enzo Maresca.

Leave a Reply