Sojoji sun nemi goyon bayan ƴan Najeriya wajen yaƙar ta’addanci

0
157

Sojoji sun nemi goyon bayan ƴan Najeriya wajen yaƙar ta’addanci

Rundunar Sojin Najeriya ta bukaci tallafin ‘yan kasa domin samun nasarar murkushe ‘yan ta’adda da sauran barazanar tsaro.

Babban hafsan Sojan ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana hakan a Taron alaka Tsakanin Sojoji da Fararen Hula na na ƙarshen shekarar 2025, a Jos, Jihar Filato.

Shaibu ya jaddada muhimmancin kafafen yada labarai wajen bayar da rahotanni na gaskiya da daidaito kan ayyukan rundunar soji, da kuma gujewa yada labaran karya da suka shafi tsaro.

KU KUMA KARANTA: Dole sojojin Najeriya su koyi harsunan gida don samun sahihan bayanan sirri — COAS

Ya kara da cewa, duk wani bayani da zai iya janyo rikice-rikice ko barazana ga kasa ya kamata a tabbatar da sahihancinsa kafin a yada shi, musamman bayanan da ake samarwa ta fasahar AI.

Babban Kwamandan Alaka Tsakanin Sojoji da Fararen Hula, Manjo Janar Musa Etsu-Ndagi, ya ce rundunar za ta ci gaba da samar da sahihan bayanai ga kafafen yada labarai domin inganta fahimtar juna da hadin kai a tsakanin sojoji da jama’a.

Taron ya mayar da hankali kan yadda rundunar soji da kafafen yada labarai za su hada kai wajen magance kalubalen tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya a kasa.

Leave a Reply