Gwamnatin Katsina ta gayyaci Shaikh Masussuka bisa zarge-zarge a karatuttukan sa

0
107

Gwamnatin Katsina ta gayyaci Shaikh Masussuka bisa zarge-zarge a karatuttukan sa

Gwamnatin Jihar Katsina ta gayyaci malamin addinin musulunci, Yahaya Masussuka, bisa zargin yin izgilanci ga shari’ar Musulunci a karatuttukan sa na yau da kullum.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Faskari, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaransa, Ibrahim Almu-Gafai, ya fitar a Katsina, ranar Talata.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta sha samun korafe-korafe cewa koyarwa da wa’azin da Masussuka yake yi sun saba wa manyan ka’idojin Shari’ar Musulunci.

Ya yi bayanin cewa, “Gwamnati ta kuma karɓi wani ƙorafi daga ɓangaren Masussuka cewa wasu mambobin Jama’atu Izalatil Bid’a suna zaginsa tare da barazanar kai masa hari.

KU KUMA KARANTA: Zargin ɓatanci ga Annabi (SAWW): Gwamnatin Kano ta ba da umarnin miƙawa Majalisar Shurah ƙorafe-ƙorafe kan Malam Lawan Triumph

“Domin warware matsalolin, an miƙa waɗannan batutuwa ga Majalisar Masarautar Katsina, inda aka gayyaci ɓangarorin biyu domin tattaunawa.

“A ƙarshen zaman, Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, ya ja hankalin cewa ba a yarda kowa ya yi wa’azi ko koyarwa ta yadda za ta cin zarafi ko tayar da hankalin wani ba.

“Don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai, Gwamna Dikko Radda ya umurci Masussuka da ya shirya domin kare kansa kan zarge-zargen, gaban Kwamitin Malamai.”

A cewar Mista Faskari, daga yanzu za a kafa ƙa’idoji da tsare-tsare na gudanar da wa’azi, yana mai jan kunne cewa “duk wanda ya keta waɗannan ƙa’idojin, gwamnati za ta ɗauki mataki na dacewa a kansa.”

Sakataren gwamnatin jihar ya kuma yi kira ga jama’a da su yi haƙuri domin ana tafiyar da batun cikin adalci da hikima.

Leave a Reply