Wata soja ta yi wuf da Sanata Kawu Sumaila

0
148
Wata soja ta yi wuf da Sanata Kawu Sumaila
Ango Sanata Kawu Sumaila da Amaryarsa Soja

Wata soja ta yi wuf da Sanata Kawu Sumaila

Sanatan mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, ya auri Aisha Isah, wata jami’ar soja da ke aiki a rundunar Sojin Saman Najeriya.

Daily Trust ta rawaito cewa an ɗaura auren ne a fadar Sarkin Rano da ke Jihar Kano a jiya Litinin da safe.

Mataimaki na musamman ga Kawu Sumaila kan yada labarai, Muttaqa Babire, ya tabbatar da wannan labari a wani rubutu da ya wallafa a Facebook, inda ya wallafa hoton sanatan tare da amaryarsa wacce ke sanye da kayan soji.

KU KUMA KARANTA: Kawu Sumaila Ya canza sheƙa daga Jam’iyya NNPP Zuwa APC

Shi ma wani mataimaki nasa, Ahmad Tijjani Salisu Kiru, ya wallafa: “JUST IN: Alhamdulillah, yau 17-11-2025, Sanata S.A. Kawu Sumaila OFR PhD ya ɗaura aure a Rano. Allah ya albarkaci wannan aure ya bada zuriya ta gari.”

Babu wata sanarwa a bayyane kafin auren, kuma hotunan daga wurin sun nuna cewa ba a yi gaiya wajen daura auren ba.

Leave a Reply