Za a yi asarar kusan Tiriliyan 2 idan aka haramta sayar da giya ‘yar leda – MAN
Daga Jameel Lawan Yakasai
Ƙungiyar Masana’antun Najeriya (MAN) ta roƙi Majalisar Dattawa da ta janye shirin haramta samarwa da sayar da giya a cikin sachet da ƙananan kwalaben PET daga ƙarshen shekarar 2025.
Darakta janar na MAN, Segun Ajayi-Kadir, ya bayyana cewa wannan mataki zai iya haddasa asarar jarin da ya kai N1.9 tiriliyan da kuma korar ma’aikata fiye da 500,000 kai tsaye da ayyuka miliyan biyar a hanya ta daban-daban.
KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar likitocin Najeriya ta yaba wa Gwamna Abba bisa gyara asibitoci 200 a Kano
Ya ce matakin zai lalata masana’antun cikin gida, rage kudaden shiga, da kuma ƙarfafa safarar giyar bogi mara tsabta.
MAN ta kuma yi kira ga Majalisar Dattawa da ta hana Hukumar NAFDAC aiwatar da haramcin daga ranar 31 ga Disamba, 2025, tare da jaddada goyon bayanta ga wayar da kai kan shan giya cikin kima da hana yara ƙanana amfani da ita.









