Shugaba Tinubu ya sake naɗa Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake naɗa Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya a matsayin shugaban hukumar yaƙi da sha da safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA.
Shugaban ya sake naɗa Marwa ne bisa jajircewarsa a da a ke samun nasara wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya.
KU KUMA KARANTA: NDLEA a Kano ta kama tabar wiwi da kwalaben Akurkura dubu 8
Bayo Onanuga ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar.
Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa Marwa a matsayin shugaban hukumar a shekarar 2021.









