An gudanar da taron ranar masu ɗaukar hoton jinya ‘Radiographers’ a Yobe

0
143
An gudanar da taron ranar masu ɗaukar hoton jinya 'Radiographers' a Yobe

An gudanar da taron ranar masu ɗaukar hoton jinya ‘Radiographers’ a Yobe

Ƙungiyar masu ɗaukar hoton jinya ta Najeriya (Radiographers), reshen jihar Yobe sun gudanar da taron ranar tunawa da ‘World Radiography Day’ a Potiskum jihar Yobe, kamar yadda suka saba kowace shekara.

A bana taron ya fara ne da ziyarar makarantun Sakandire, irinsu FECOET Potiskum, FGGC Potiskum da FGC Buni Yadi don wayar da kan ɗaliban a kan muhimmancin karanta Radiography a jami’o’i, saboda amfaninsa ga al’umma.

Sannan sun yi wa mata sama da 200 scanning kyauta, a Asibitin ƙwararru na jihar Yobe da ke Potiskum. Sannan sun yi tafiya a ƙafa, tun daga Asibitin ƙwararru na jihar Yobe da ke Potiskum har zuwa bakin babbar kasuwar Potiskum. Suna tafe suna tafe suna bayyana wa jama’a cewa ” Yau ce ranar masu ɗaukar hoton jinya’ ta duniya’ (World Radiography Day).

KU KUMA KARANTA: Rashin ƙiba a yara na iya zama alamar tarin fuka – Masana

Daga nan sai aka wuce ɗakin taro na Annoor Hotel da ke Potiskum, inda aka gudanar da taro na musamman don tuna wa da wannan rana.
Dakta Mohammed Abba daga Jami’ar Bayero Kano, shi ne ya kasance babban baƙo mai jawabi a wajen. Dakta Abba ya yi jawabi ne mai taken ‘amfani da gudumawar Radiographers da ci gaban da ya kawo a harkar kiwon lafiya’.

Ya taɓo ɓangarori da dama da suka shafi nasarori da bunƙasar karanta Radiography a manyan jami’o’i. Sannan ya sauƙaƙa hanyoyin gano cuta da ta ɓuya a jikin mutum.

An karrama mutane 4 a wajen, waɗanda suka ba da gagarumar gudumawa a ci gaban harkar kiwon lafiya a jihar Yobe. Waɗanda aka karrama ɗin sun haɗa da;
1. Hon. Ajiya Maina Kachalla (Ɗan majalisa mai wakiltar Machina) kuma shugaban kwamitin kiwon lafiya a majalisar dokokin jihar Yobe.
2. Hon. Engineer Saminu Musa Lawan (Ɗan majalisa mai wakiltar Nangere)
3. Hon. Ahmed Adamu BBK (Ɗan majalisa mai wakiltar Potiskum).
4. Dr. Zakari Usman (Medical Director) Yobe State Specialist Hospital Potiskum.

Manyan baƙi a wajen sun haɗa da, wakilin mai martaba Sarkin Fika da wakilin mai martaba Sarkin Potiskum, CMAC Dakta Sadik Abubakar Zakari, HOD Nursing, Abdullahi Jeni da sauransu.

A tattaunawarsa da manema labarai bayan kammala taron, HOD Radiography, RAD Isyaku Mu’azu ya yaba wa Gwamnan Yobe, Dakta Mai Mala Buni CON, bisa ga yadda yake ƙoƙari matuƙa a kan harkar kiwon lafiya a jihar Yobe. Sannan ya koka a kan rashin mashin na yin scanning, mai suna ‘City Scan’ da sauran kayayyakin aiki a ɓangaren Radiography na Asibitin ƙwararru na jihar Yobe da ke Potiskum.

Leave a Reply