Ɗan wasan Kannywood Malam Nata’ala ya rasu
Allah Ya yiwa shahararren ɗan wasan Kannywood na shirin Daɗin Kowa, Malam Nata’ala rasuwa.
Malam Nata’ala ya yi fama da doguwar jinya.
KU KUMA KARANTA: Wace cuta ce ke damun Malam Nata’ala na shirin Daɗin Kowa?
Ya rasu yau Lahadi a Asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri. Za a kawo shi Potiskum a yi masa Sallar jana’iza.
Zuwa yanzu ba a saka lokacin jana’iza ba.









