No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hisbah ta kama mutane 25 bisa zargin shirya auren jinsi a Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama akalla mutane 25 bisa zargin shirya auren jinsi a unguwar Hotoro da ke cikin birnin Kano.

Mataimakin Kwamandan Hukumar, Mujahedeen Aminudeen, ne ya tabbatar da kamun a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Lahadi.

A cewarsa, jami’an hukumar sun cafke wadanda ake zargin — maza 18 da mata bakwai — a cibiyar taro ta Fatima Event Centre da ke kan hanyar Hotoro Bypass a ranar Asabar.

KU KUMA KARANTA: Hisbah ta soke auren Idriss Mai Wushirya da Basira ‘Yar Guda

“Yau Asabar, 25 ga Oktoba, 2025, mun samu rahoton cewa wasu mutane na shirin yin auren ‘Jinsi. Nan take jami’anmu suka dira cibiyar taron Fatima Event Centre, inda aka shirya wannan haramtaccen taron, kuma suka kama mutane 25,” in ji Aminudeen.

Ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin, ciki har da wanda ake kira ango, daga yankuna daban-daban kamar Sheka, Yar Gaya, da Kofar Nasarawa.

Mataimakin Kwamandan ya gargadi cewa hukumar ba za ta zauna ba ta bar wasu marasa tarbiyya su bata sunan Kano ba.

“Muna kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da baiwa hukumar hadin kai ta hanyar kawo rahoton duk wani abu da ya shafi rashin tarbiyya a cikin al’umma. Hukumar Hisbah za ta ci gaba da kai samame a wuraren da ke yada alfasha,” in ji shi.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...