No menu items!

Sample Page Title

Date:

KANFEST 2025: Gwamna Kano ya umarci sarakunan Kano da su ci gaba da hawan sallah

Daga Jameel Lawan Yakasai

Domin tabbatar da ci gaba da adanawa da kuma yada al’adun gargajiya na Jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci dukkanin Sarakunan jihar da su ci gaba da gudanar da bikin hawan sallah a kowacce shekara.

Gwamna Yusuf ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta ba da cikakken goyon baya ga masarautu domin tabbatar da cewa wannan tsohuwar al’ada ta ɗore, ta ƙara ƙarfi, kuma a nuna ta ga duniya baki ɗaya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a wajen bude taron KANFEST (Kalankuwa) 2025, wanda aka shirya domin nuna ɗimbin al’adun Kano da ƙarfafa masu fasaha, da haɗa kan matasa da mata tare da gina haɗin gwiwa ta duniya wacce za ta ɗora Kano a taswirar al’adu ta duniya.

KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘yansanda ta hana hawan Sallah a Kano

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Kano kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar, Dr. Muhammadu Sanusi II, ya yabawa hangen nesa na Gwamnatin Jihar Kano wajen dawo da girmamawa ga al’adun mutanen Kano waɗanda suka taɓa dusashewa.

Wannan biki na kwanaki uku zai ƙunshi nunin al’adu da abincin gargajiya da wasan kwaikwayo da wasanni, da kayan ɗinki da tukwane da gabatar da makalu daga masana.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...