‘Yansanda sun sake cafke Sowore bayan kotu ta ba da belinsa

0
132
'Yansanda sun sake cafke Sowore bayan kotu ta ba da belinsa
Omoyele Sowore

‘Yansanda sun sake cafke Sowore bayan kotu ta ba da belinsa

Rundunar Ƴansandan Najeriya ta sake kama tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Omoyele Sowore, sa’o’i kaɗan bayan wata kotun majistare ta bada belinsa.

An bada belin Sowore da wasu masu zanga-zanga fiye da goma sha biyu, bayan da aka kama su a ranar 20 ga Oktoba yayin zanga-zangar adawa da ci gaba da tsare shugaban ƙungiyar IPOB mai fafutukar kafa Biafra, Nnamdi Kanu.

KU KUMA KARANTA: Sowore da Ɗan Bello sun jagoranci jami’an ‘yansanda da suka yi ritaya zanga-zanga, duk da gargaɗin da aka yi musu

Rahotanni sun bayyana cewa Sowore da mutum 12, ciki har da ɗan’uwan Nnamdi Kanu mai suna Prince Emmanuel Kanu, an kama su ne tun farkon makon nan.

A wata sanarwa da lauyoyinsa suka fitar, sun bayyana sake kama Sowore a matsayin “wulakanci ga tsarin doka” da kuma take hakkin ɗan adam.

Rundunar ‘yansanda dai har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa game da dalilan da suka sa suka sake kama shi ba har zuwa lokacin da ake wannan rahoton.

Leave a Reply