No menu items!

Sample Page Title

Date:

Mun mayar da Kano ta zama cibiyar kasuwanci ta yankin Sahel — Gwamna Yusuf

Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya bayyana cewa cikin sauri jihar Kano na zama babbar cibiyar kasuwanci ta yankin Sahel, sakamakon sauye-sauyen da aka aiwatar tare da janyo masu zuba hannun jari.

Gwamnan, wanda mai ba shi shawara kan harkokin jiha, Alhaji Usman Bala, ya wakilta a wajen kaddamar da littattafai biyu a Abuja, ya jaddada cewa gwamnatin sa na amfani da tarihin kasuwancin Kano tare da rungumar sabbin hanyoyin kasuwanci na zamani.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya canza kwamishinan shari’a

Ya ce gwamnatinsa ta dauki matakan farfado da tattalin arziki ta hanyar inganta tsaro, i’ababen more rayuwa, da bunkasa wutar lantarki.

Haka kuma, ya bayyana cewa an fara aikin sauya tsarin karbar kudaden shiga zuwa na zamani da kuma toshe hanyoyin salwantar kudade.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...