Gwamnatin Filato ta kama ‘yar fafutuka saboda fallasa gazawar gwamnati – ‘Yan Najeriya na sukar matakin
Rahotanni daga birnin Jos sun tabbatar da cewa jami’an tsaro a ranar Talata sun kama Ummulkhair Abdulmumin Iliyasu, wata matashiya ‘yar fafutuka kuma mai amfani da kafafen sada zumunta wajen bayyana matsalolin da al’umma ke fuskanta a jihar Filato, musamman a cikin ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
Lauyan ta da ya tabbatar wa da Neptune Prime faruwar lamarin ya bayyana cewa kama Ummulkhair ya biyo bayan wallafe-wallafen da take yi a dandalin Facebook inda take bayyana gazawar gwamnati wajen samar da ingantattun ayyuka, tsaro da kula da matasa a yankin.
Majiyoyi sun ce jami’an tsaron ƴan sandan jahar Filato a sashin binciken manyan lefuka sun kai farmaki gidanta ne inda basu sameta ta ba sai suka gayyace ta, inda nan take ta amsa gayyatar tare da ayarin lauyoyin ta.
A ofishin nasu, sun nemi ta goge dukkan bidiyon da ta yi tana sukar gwamnatin Filato da shugaban ƙaramar hukumar Jos ta Arewa tare da basu haƙuri. Lamarin da ya sa lauyoyin ta suka turɓune suka ce, hakan ba mai faruwa bane domin kuwa gaskiya ta faɗa bata yi ƙage ga kowa ba.
An hangi shugaban ƙaramar hukumar Jos ta Arewa Barr. JK Chris yana ta zarya a ofishin shugaban ƴan sandan jahar Filato inda ya buƙaci sai an kulle Ummulkhair.
KU KUMA KARANTA: Hukumar SSS za ta ladabtar da jami’an ta da suka kama tare da tsare ‘yan jarida a Jos
Bayan tsare ta na dogon lokaci, lauyan ta ya nemi belin ta inda aka ba shi kuma aka ce su koma yau Talata domin ci gaba da tuhumar da ake mata.
Ƴan Najeriya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun yi martani
Masu kare hakkin bil’adama a kafafen sada zumunta irin su Abba Hikima, Ɗan Bello, Human Rights Watch Nigeria, Amnesty International Nigeria, da wasu ‘yan fafutuka a Jos da lungu da saƙon Najeriya sun bayyana cewa kama Ummulkhair cin zarafi ne ga ‘yancin faɗar albarkacin baki kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada a sashe na 39.
Wata sanarwa da ƙungiyar Centre for Civic Freedom (CCF) ta fitar ta ce:
“Kama Ummulkhair saboda ta bayyana ra’ayinta kan yadda gwamnati ke gudanar da mulki, babban abin damuwa ne. Wannan lamari na iya zama barazana ga sauran matasa masu rajin gaskiya a jihar Filato.”
Gwamnatin Filato Da Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa Basu Ce Komai Ba Game Da Lamarin
Kawo yanzu, gwamnatin Filato da shugaban ƙaramar hukumar Jos basu ce komai game da lamarin ba inda matasa suke zargin da hannunta wajen wasu maƙarraban gwamnati wajen kama ƴar fafutukar.
Kiran Neman Adalci
A halin yanzu, ana kiran gwamnatin Filato ƙarƙashin Caleb Mutfwang da Shugaban Karamar hukumar Jos ta Arewa Barr JK Chris su saki Ummulkhair nan da nan tare da binciken adalci kan yadda aka yi gumurzu wajen kama ta.
Kammalawa
Kama Ummulkhair Iliyasu Abdulmumin ya sake tayar da muhawara kan irin matsin lamba da masu fafutuka da ‘yan jarida ke fuskanta a Najeriya, musamman idan suka fallasa gazawar gwamnati ko shugabanni.
Masana na ganin cewa irin waɗannan abubuwa na iya ta’azzara rashin yarda tsakanin gwamnati da jama’a, idan ba a bi hanyoyin dimokuraɗiyya wajen magance su ba.
Auwal Saleh
Jos, Filato.
7 ga Oktoba, 2025.









