Uwargidan shugaban ƙasa ta raba jarin Naira miliyan 25 ga mata 500 a Katsina

0
157
Uwargidan shugaban ƙasa ta raba jarin Naira miliyan 25 ga mata 500 a Katsina

Uwargidan shugaban ƙasa ta raba jarin Naira miliyan 25 ga mata 500 a Katsina

Uwargidar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Tony Elumelu, ta rabawa mata masu ƙananan sana’o’i 500 jari na Naira miliyan 25 a Jihar Katsina, inda kowacce mace ta samu Naira dubu 50.

An gudanar da taron rabon tallafin ne a yau Litinin a Katsina , da nufin bunƙasa tattalin arziki a matakin ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Uwargidan shugaban ƙasa ta bayar da tallafin kuɗi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Abuja

A yayin raba kuɗaɗen, uwargidar Gwamnan Jihar Katsina, Zulaihat Radda, ta ce shirin na da matuƙar muhimmanci ga al’umma.

“An kaddamar da wannan shiri a jihohi daban-daban na ƙasar nan domin tabbatar da cewa mata sun samu tallafin da suke buƙata don gina kyakkyawar makoma, ” in ji ta

Leave a Reply