Hukumar Shari’a ta Kano ta dakatar da buɗe sabon masallacin Juma’a a Sharaɗa

0
213
Hukumar Shari’a ta Kano ta dakatar da buɗe sabon masallacin Juma’a a Sharaɗa

Hukumar Shari’a ta Kano ta dakatar da buɗe sabon masallacin Juma’a a Sharaɗa

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Shari’a ta jihar Kano ta dakatar da buɗe sabon masallacin Juma’a da aka gina a gidan marigayi Alhaji Ghali Umar Na’abba, da ke kan titin Sharaɗa kusa da hedikwatar hukumar Hisbah.

A cewar hukumar, dakatarwar ta biyo bayan karya dokokin tantance masallatan Juma’a da sahalewar buɗewa a jihar.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun shugaban ta, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bisa tanade-tanaden dokar tantance masallatan Juma’a ta shekarar 2003.

KU KUMA KARANTA: Ƙudan zuma sun kusa hana sallar jumu’a a Potiskum

Sheikh Daneji ya ce, baya ga rashin bin ka’ida, masallacin ya yi kusa da hedikwatar hukumar Hisbah, inda suka kasance a katanga ɗaya, abin da ya saba da tsarin da doka ta tanada.

Sanarwar ta ƙara da cewa an tura takardar dakatarwar zuwa ofishin mataimakin babban sufeton ƴansanda mai kula da shiyya ta ɗaya (Zone One), rundunar ƴan sanda ta jihar Kano, fadar mai martaba Sarkin Kano, Ma’aikatar Harkokin Addinai ta jihar, da kuma ofishin hukumar tsaron farin kaya ta ƙasa (DSS), reshen Kano, domin a duba batun.

Leave a Reply