Gwamna Abba Kabir ya nemi shugaban ƙasa Tinubu ya sauya kwamishinan ‘yansandan Kano saboda rashin iya aiki
Daga Jameel Lawan Yakasai
Gwamnan Jihar Kano, Alh. Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta sauya kwamishinan ‘yan sanda na jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai, inda ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda kwamishinan ya janye jami’an tsaro daga filin wasa na Sani Abacha lokacin taron.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya canza kwamishinan shari’a
Ya ce wannan mataki bai dace ba, kuma ka iya barazana ga tsaro da zaman lafiya a lokacin da ake gudanar da muhimmin bukin kasa.









