Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi
Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta sanar da dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi.
A wani taron manema labarai da Sakataren majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi a ranar Laraba, ya ce an dakatar da Malam Lawan ne domin bashi damar ya zo gaban majalisar ya kare kansa daga zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman ɓatanci ga Ma’aiki (SAWW).
KU KUMA KARANTA: Zargin ɓatanci ga Annabi (SAWW): Gwamnatin Kano ta ba da umarnin miƙawa Majalisar Shurah ƙorafe-ƙorafe kan Malam Lawan Triumph
A cewar Sagagi, an dakatar da Malam Lawan har sai an kammala bincike da jin ta bakinsa a matakin Majalisar ta shura.
Ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su guji tsoma baki a batun, inda ya buƙaci da a ƙyale kwamitin ya kammala aikinsa.
Sagagi ya tabbatar da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da don rai ko rashin adalci ba.









