No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta sanar da Naira miliyan 8.2 a matsayin kuɗin aikin hajjin baɗi

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince da Naira miliyan 8.2 a matsayin kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026.

Daraktan Hukumar, Lamin Danbappa, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Sulaiman Dederi, ya fitar a ranar Asabar a Kano.

Danbappa ya bayyana cewa kuɗin sun yi daidai da umarnin Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) kuma sun shafi dukkan masu niyyar zuwa aikin hajji.

Ya ce masu niyyar zuwa aikin hajji da suka riga suka ajiye Naira miliyan 8.5 za a mayar musu da ragowar kuɗin bayan sun rubuta takardar neman a maida musu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa, masu niyyar zuwa aikin hajji da za su fara biyan kuɗi yanzu ana sa ran su biya Naira miliyan 8.2 bisa ga umarnin da aka amince da shi.

KU KUMA KARANTA: Hukumar jindaɗin Alhazai a Kano ta fara raba kayan aikin Hajjin bana

Danbappa ya ƙara da cewa, ranar ƙarshe ta biyan kuɗin ita ce 31 ga Disamba, 2025, inda ya shawarci masu niyyar zuwa aikin hajji da su kammala biyan kuɗaɗen kafin lokacin domin tabbatar da gurbin tafiyarsu.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...