NRC ta sanar da tana dab da dawo da jigilar jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja

0
112

NRC ta sanar da tana dab da dawo da jigilar jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja

Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa jirgin ƙasa mai zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna zai dawo aiki a mako mai zuwa.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Callistus Unyimadu, ya fitar ranar Asabar, inda ya bayyana cewa an kammala gyaran sashen layin dogo da ya lalace a Asham, Kaduna.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta sanar da lokacin kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano

Unyimadu ya ce hukumar ta riga ta mayar wa da kuɗin tikiti fasinjoji 512 daga cikin 558 da ke cikin jirgin da abin ya rutsa da su. Ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin tuntubar sauran domin a biya su.

Ya bayyana cewa hukumar za ta sanar da takamaiman ranar komawa aiki da jadawalin tafiye-tafiye a cikin kwanaki masu zuwa.

Leave a Reply