An shirya taron tunawa da shekaru 20 da rasuwar Yusuf Bala Usman a Zariya

0
185
An shirya taron tunawa da shekaru 20 da rasuwar Yusuf Bala Usman a Zariya

An shirya taron tunawa da shekaru 20 da rasuwar Yusuf Bala Usman a Zariya

Daga Idris Umar, Zariya

An gudanar da taron tunawa da Dakta Yusuf Bala Usman, wanda aka fi sani da marubuci kuma masanin tarihi, wanda ya rasu shekaru 20 da suka wuce. Cibiyar da aka kafa da sunansa – Yusuf Bala Usman Centre da ke GRA Zariya jihar Kaduna ce ta shirya wannan taron domin tunawa da irin gudummawar da ya bayar a rayuwarsa.

Taron ya tara masana daga sassa daban-daban na Najeriya da kasashen waje, inda kimanin mutane 12 suka gabatar da kasidu masu muhimmanci, musamman a fannin tarihi, siyasa da zamantakewar al’umma.

Daga cikin fitattun wadanda suka gabatar da jawabi akwai Farfesa Attahiru Jega, wanda ya taba rike matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa. Ya yi magana ne kan zabe da siyasar Najeriya a halin yanzu. A cikin jawabin nasa, ya yaba da irin namijin kokarin da Yusuf Bala ya yi wajen yaki da zalunci da kuma fadakar da jama’a. Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayin tare da albarkaci zuriyarsa.

Haka kuma, tsohon ɗan jarida daga jihar Jigawa, Malam Sani Zarro, ya yi kira ga malamai da su yi koyi da irin halayyar Yusuf Bala. Ya ce yana daga cikin mutanen da suka tsaya kan gaskiya, suka ki zalunci, suka kuma nemi sauyi na gari a Najeriya. Zarro ya bukaci cibiyar da ta shirya taron da ta ci gaba da kokari, musamman wajen amfani da kafafen watsa labarai domin yada irin sakonnin da Yusuf Bala ke fadakar da mutane da su a lokacin rayuwarsa.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar marubuta ta Alƙalam za ta yi taron tunawa da marubuci marigayi Mahmoon Baba-Ahmed

Wanda ya jagoranci taron shi ne Malam Ibrahim Mu’azzam daga Center for Research and Documentation, Kano.

Daga cikin wadanda suka san Yusuf Bala kai tsaye ko kuma suka yi aiki tare da shi, akwai mutane kamar su Ambassador Abdu A. Zango, Farfesa Watsi O. Alli, Farfesa Jibrin Ibrahim, Dakta Auwalu Anwar, Dakta Iyorchia Ayu, Oluwatosin Orimolade, Dakta Sama’ila Ibrahim da sauransu. Kowannensu ya bayyana irin yadda marigayin ya ba da gudummawa wajen ilimi da tarbiyyar matasa.

A ƙarshe, an kammala taron lafiya, an tashi lafiya, cikin girmamawa da tunawa da mutum mai tarihin nagarta kamar Yusuf Bala Usman.

Leave a Reply