Mutane sama da 20 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato 

0
118
Mutane sama da 20 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato 

Mutane sama da 20 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato

Mutane goma ne aka tabbatar da rasuwarsu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya faru a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Rahotanni sun ce jirgin ruwan na ɗauke da mazauna garin Zalla-Bango da ke tserewa daga harin ‘yan bindiga.

A cewar Zagazola Makama, wata jarida mai wallafa rahotannin yaƙi da ta’addanci, rundunar ‘yansanda ta tabbatar da lamarin a ranar Asabar, inda ta ce jirgin ya kife da fasinjoji 10, dukkansu kuma suka nutse.

KU KUMA KARANTA: Kifewar jirgin ruwa ta kashe mutane da dama a jihar Sokoto

Majiyoyi sun bayyana cewa daga bisani aka gano gawarwakin da misalin ƙarfe 11:30 na safe a ranar Alhamis, bayan bincike mai zurfi da mazauna ƙauyen tare da masunta suka gudanar.

Wannan lamari ya faru ne makwanni kaɗan bayan wani hatsarin jirgin ruwa a Garin-Faji, cikin ƙaramar hukumar Sabon-Birni, inda mutum fiye da biyar suka mutu, yayin da aka ceto mutum 21.

Hakazalika, mako guda kafin wannan, wani hatsarin jirgin ruwa ya faru a ƙauyen Kojiyo, cikin ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar.

A duka lokutan, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), tare da wasu hukumomi ciki har da Hukumar Ruwa ta Ƙasa (NIWA) da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Sokoto, sun kasance cikin Sahun farko da suka isa wajen bada agaji.

Leave a Reply