Jami’in NSCDC a Kano ya tsinci kuɗi sama da Naira Miliyan 20, ya mayar wa mai shi

0
377
Jami'in NSCDC a Kano ya tsinci kuɗi sama da Naira Miliyan 20, ya mayar wa mai shi

Jami’in NSCDC a Kano ya tsinci kuɗi sama da Naira Miliyan 20, ya mayar wa mai shi

Daga Jameel Lawan Yakasai

Wani matashi jami’in rundunar tsaro ta Civil Defense a jihar Kano, mai suna Nura Abdullahi, dan asalin jihar Katsina, ya mayarwa wani mutum wasu tarin kudade da suka tasamma Naira Miliyan 20, da ya tsinta a cikin baburi mai kafa uku na adai-daita sahu.

Da yake zantawa da Jaridar Neptune Prime a Kano, mamallakin kuɗin ɗan asalin jihar Katsina, ya bayyana jin daɗin sa, inda ya ce akwai buƙatar gwamnatin jihar Kano, da ta Katsina su karrama matashin jami’in rundunar tsaron ta Civil Defense, bisa yadda ya nuna gaskiya.

KU KUMA KARANTA: An karrama matashin da ya tsinci dala 10,000 a Kano

Musamman cikin wannan yanayi da ake ciki na talauci, da karajin tausayawa juna, amma wannan mutumi ya yi na mijin kokari ya ɗauke zuciyar sa ya mayar da hakkin da banasa ba.

A karshe ya yi godiya da addu’oi ga wannan jami’in Civil Defense.

Leave a Reply