‘Yansanda a Yobe sun kama wanda ake zargi da yi wa ƙananan yara fyaɗe, sun jaddada aniyar daƙile cin zarafin mata

0
245
‘Yansanda a Yobe sun kama wanda ake zargi da yi wa ƙananan yara fyaɗe, sun jaddada aniyar daƙile cin zarafin mata
Kwamishinan 'yansandan jihar Yobe Emmanuel Ado

‘Yansanda a Yobe sun kama wanda ake zargi da yi wa ƙananan yara fyaɗe, sun jaddada aniyar daƙile cin zarafin mata

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta kama wani matashi ɗan shekara 22 mai suna Ishiaku Bukar da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 11 fyaɗe a ƙauyen Maiduwa da ke ƙaramar hukumar Fika ta jihar.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya fitar, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar, 13 ga watan Satumba, 2025, biyo bayan kiran waya da ‘yan uwar yarinyar suka yi.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Zariya, sun kama matashi ɗan ƙabilar Ibo da zargin fyaɗe

Binciken farko da aka yi ya nuna cewa wanda ake zargin ya yaudari yarinyar zuwa gonarsa da sunan neman taimakonta, inda ya yi alƙawarin zai ba ta kuɗi, amma sai ya yi amfani da wannan dama, ya aikata wannan ɗanyen aikin.

Sanarwar ta ce “Wanda ake zargin ya amsa laifinsa yayin da ake yi masa tambayoyi, ana ci gaba da gudanar da bincike yayin da ita kuma yarinyar ke samun kulawar lafiya,” in ji sanarwar.

Rundunar ta kuma nuna matuƙar damuwarta kan ƙaruwar rahotannin cin fyaɗe da cin zarafin mata da ƙananan yara da ake yi a matsayin masu aikin gona. Yayin da ake ci gaba da gudanar da noma a faɗin jihar, rundunar ‘yan sandan ta yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da irin wannan laifin za a hukunta shi mai tsanani kamar yadda doka ta tanada.

KU KUMA KARANTA: An tsinci gawar ’yar shekara 2 bayan an yi mata fyaɗe

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya tabbatar da matakin da rundunar ta ɗauka na nuna rashin amincewa da fyaɗe da cin zarafin mata, inda ya buƙaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi.

Rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga ɗaukacin mazauna yankin da su ba da goyon baya don yaƙar cin zarafin mata da kuma kare masu mutunci a cikin al’umma.

Leave a Reply