Idan ba a yi wasa ba Tinubu zai fara ciyo bashi a Opay da Moniepoint da Palmpay – Dino Melaye

0
184
Idan ba a yi wasa ba Tinubu zai fara ciyo bashi a Opay da Moniepoint da Palmpay - Dino Melaye
Sanata Dino Melaye

Idan ba a yi wasa ba Tinubu zai fara ciyo bashi a Opay da Moniepoint da Palmpay – Dino Melaye

Daga Jameel Lawan Yakasai

Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yadda take ci gaba da ciyo basussuka daga ƙasashen waje da cibiyoyin kuɗi, yana mai gargadi cewa lamarin na iya kaiwa ga neman bashi daga kamfanonin kuɗin intanet kamar Opay da Moniepoint.

Melaye ya yi wannan magana ne a wata hira da tashar talabijin ta Arise a ranar Litinin, inda ya zargi gwamnatin da jefa ’yan ƙasa cikin mawuyacin hali saboda basussukan da ya ce ba sa amfani wa talakawa ba.

KU KUMA KARANTA: Yawaitar bashin da Najeriya ke karɓowa abin damuwa ne – Tajuddeen Abbas

Ya tambayi dalilin da yasa Shugaban ƙasa zai nemi bashi na dala biliyan 1.7 daga Bankin Duniya, yayin da Majalisar Dattawa ta riga ta amince da basussuka da suka kai sama da dala biliyan 21, tare da ƙarin wasu da ke kan hanya.

Melaye ya kuma bayyana gwamnatin a matsayin “mafi sakaci a tarihin Najeriya”, yana mai cewa duk da samun kuɗaɗen shiga, har yanzu ana ƙara dogaro da bashi.

Ya yi gargadin cewa, “ba abin mamaki ba idan nan gaba gwamnati ta koma neman bashi daga Opay da Moniepoint.”

Leave a Reply