Wike ya ci tarar Ganduje, Idiagbon da Oyinlola kan amfani da filaye ba bisa ƙa’ida ba

0
243
Wike ya ci tarar Ganduje, Idiagbon da Oyinlola kan amfani da filaye ba bisa ƙa’ida ba

Wike ya ci tarar Ganduje, Idiagbon da Oyinlola kan amfani da filaye ba bisa ƙa’ida ba

Daga Jameel Lawan Yakasai

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ci tarar wasu manyan ’yan siyasa da jami’an gwamnati Naira miliyan 5 saboda sauya filayen da aka ba su zuwa wani amfani daban ba tare da izini ba.

Masu laifin sun haɗa da tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, tsohon shugaban ma’aikata na Supreme Headquarters a zamanin Babangida, marigayi Janar Tunde Idiagbon, tsohon gwamnan Osun Prince Olagunsoye Oyinlola, da tsoffin manyan alkalai na ƙasa, Justice Atanda Fatai-Williams da Justice Aloma Mariam Mukhtar.

KU KUMA KARANTA: Ba za mu daina rusau a Abuja ba – Wike 

Ma’aikatar birnin tarayya ta Abuja ta ce Ganduje ya sauya gida a Wuse 2 zuwa banki, Idiagbon ya maida gida a Maitama zuwa otal, yayin da Oyinlola ya maida gida a Asokoro zuwa Zhouyi Hotel.

Haka kuma an gano wasu sun maida kadarorin su zuwa kasuwanni, otal-otal, wuraren baje kolin kaya, dakin motsa jiki da kantin sayarwa.

Wike ya umarci duk wanda abin ya shafa da su biya tarar kafin 10 ga Satumba, 2025, tare da sabunta takardun filayen su bisa sabon tsarin amfani da filaye na shekara 99.

Leave a Reply