Talauci da rashin aikin yi ne ya haifar da rashin tsaro a Arewa — Uba Sani

0
116
Talauci da rashin aikin yi ne ya haifar da rashin tsaro a Arewa — Uba Sani
Gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani

Talauci da rashin aikin yi ne ya haifar da rashin tsaro a Arewa — Uba Sani

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayyana cewa talauci, rashin aikin yi, karancin makarantu, asibitoci da harkokin kasuwanci a yankunan karkara ne tushen aikata laifuka, inda ya jaddada cewa shugabanni dole ne su ɗauki alhakin magance matsalar.

Gwamnan ya yi wannan gargadi ne a wajen kaddamar da littafin “Where I Stand” na marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, wanda Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya fassara zuwa harshen Larabci.

Ya kuma shawarci jam’iyyun adawa da su daina siyasantar da batun tsaro da ikirarin cewa za a iya murkushe ‘yan bindiga ta hanyar yi musu ruwan bama-bamai.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kaduna zai ba da ilimi kyauta ga ɗaliban Kuriga

Gwamna Sani, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron a matsayin Babban Bako na Musamman, kuma shi ne Mai masaukin baki, ya bayyana cewa rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma ya bambanta da ta’addancin Boko Haram na Arewa maso Gabas da ke da ra’ayin addini. Ya ce a nan talauci, rashin aikin yi da sakaci da yankunan karkara su ne tushen matsalar ‘yan bindiga.

A cewar sa, “ba za a iya magance matsalar tsaro ta hanyar amfani da bindigogi kawai ba,” yana mai cewa duk wanda ya yi irin wannan ikirari yana yin siyasa ne kawai.

“Dole mu ji tsoron Allah, mu daina yaudarar mutane saboda wannan hanya ba za ta taba aiki ba,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa yawan ma’aikatan tsaro a Najeriya ya ragu duk da ƙaruwa mai yawa da aka samu a yawan jama’a cikin shekaru 45 da suka wuce.

Leave a Reply