Mutane miliyan 31 za su faɗa cikin yunwa matsananciya a Najeriya – Majalisar Ɗinkin Duniya

0
223
Mutane miliyan 31 za su faɗa cikin yunwa matsananciya a Najeriya - Majalisar Ɗinkin Duniya

Mutane miliyan 31 za su faɗa cikin yunwa matsananciya a Najeriya – Majalisar Ɗinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 31 ne ke fuskantar ƙarancin abinci a Niajeriya, wanda hakan ne mafi yawa a tarihi, sanadiyyar rage kudin tallafi da Amurka da sauran ƙasashen Yamma ke bayarwa.

Matsalar yunwar ta fi ƙamari ne a arewa maso gabashin ƙasar inda aka yi ƙiyasin cewa iyalai miliyan 2.3 suka tarwatse a cikin shekara 16 na rikicin Boko Haram.

A baya Amurka ce take bayar da kashi 60 cikin ɗari na tallafin jin-ƙai a Najeriya, sai dai shugaba Donald Trump ya dakatar da tallafin.

A yanzu ƙasashen Yamma sun mayar da hankali wajen kashe kudi kan tsaro sanadiyyar barazana daga Rasha.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya na bana ba — Fadar shugaban ƙasa

A sanadiyyar haka, ala tilas Najeriya ta zabtare kudin da take kasaftawa na tallafin jin-ƙai daga dala miliyan 910 zuwa dala miliyan 300.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikici da sauyin yanayi da matsin tattalin arziƙi da ambaliyar ruwa sun ƙara munana matsalar ƙarancin abinci.

Rashin kudi ya tilasta Shirin Samar da Abinci na MDD rufe cibiyoyinsa 150 a fadin ƙasar, lamarin da ya katse abinci ga miliyoyin al’umma tare da dakatar da kulawar lafiya da ake bai wa yara masu fama da tamowa.

Sai dai daga baya Amurka ta ce za ta bayar da tallafin kuɗi dala miliyan 32.5 ga Shirin Samar da abinci na WFP domin ci gaba da tallafa wa mutanen da rikici ya tarwatsa a Najeriyar.

Leave a Reply