Ku daina takurawa El-Rufai, ku mai da hankali kan ‘yanbindiga – Jam’iyar ADC ga ‘yansanda 

0
156

Ku daina takurawa El-Rufai, ku mai da hankali kan ‘yanbindiga – Jam’iyar ADC ga ‘yansanda

Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin tarayya da amfani da jami’an tsaro wajen tsoratar da shugabannin adawa, tana mai cewa hakan barazana ce ga dimokuradiyya.

Jam’iyyar ta yi Allah-wadai da takardar gayyatar da aka aika wa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da kuma harin da aka kai wa tawagar tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami. Ta kuma ce ’yansanda sun rufe ofishinta a Kaduna da kuma kasa kama ’yan daba da suka kai hari a tarurrukan jam’iyyar a Kaduna da Kebbi.

Kakakin jam’iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ya ce ’yansanda sun fi karkata wajen musgunawa shugabannin adawa maimakon kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa, alhali ’yan bindiga na addabar arewacin Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Mambobin ADC sun shigar da ƙara akan sabbin shugabannin riƙo na jam’iyyar

ADC ta bukaci a gaggauta soke gayyatar da aka aika wa shugabanninta, bude ofishinta a Kaduna da kuma kama wadanda suka kai hare-haren.

Jam’iyyar ta gargadi gwamnati da ’yansanda da su maida hankali kan aikin kare ’yan kasa ba siyasa ba.

A nasa bangare, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce abubuwan da ke faruwa yanzu na nuna yiwuwar Najeriya na karkata zuwa mulkin kama-karya a karkashin Shugaba Bola Tinubu.

Leave a Reply