Farfesa Hafizu Yakasai na jami’ar Bayero ya rasu
Daga Jameel Lawan Yakasai
Allah ya yiwa Farfesa Hafizu Miko Yakasai rasuwa a daren jiya Alhamis.
Farfesa Miko kafin rasuwarsa shehin malami ne a fannin nazarin harsuna na Jami’ar Bayero da ke Kano.
KU KUMA KARANTA: Mahaifin Daraktan Neptune Prime, Aisha Auyo, ya rasu
Za’a yi jana’izar shi yau Juma’a 5 ga Satumba da karfe 9 na safe a unguwar Yakasai da ke cikin birnin Kano.









