Dole mu ƙirƙiri ‘yansandan jihohi don magance matsalar tsaro a Najeriya – Tinubu

0
314
Dole mu ƙirƙiri 'yansandan jihohi don magance matsalar tsaro a Najeriya - Tinubu
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Dole mu ƙirƙiri ‘yansandan jihohi don magance matsalar tsaro a Najeriya – Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce kafa rundunar ’yan sandan jihohi ya zama dole, domin magance matsalar tsaro da ke damun ƙasar.

Tinubu ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya karɓi tawagar manyan ’yan asalin Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Radda.

Ya umarci hukumomin tsaro da su sake duba dabarun aikin su a Katsina, tare da tabbatar da rahoton yau da kullum, sannan ya sanar da amincewar gwamnati kan ƙarin sayen jiragen leƙen asiri (drones).

Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa za a tura kayan aikin soja na zamani da na’urorin sa ido a jihar, tare da duba yiwuwar ƙarfafa mafarauta da aka tura.

KU KUMA KARANTA: Matsalar tsaro na ƙara taɓarɓarewa a Najeriya – Amnesty

Tinubu ya jaddada cewa matsalar tsaro ba za ta gagari gwamnati ba, yana mai cewa: “Za mu kafa ’yan sandan jihohi, za mu magance rashin tsaro, dole mu kare ’ya’yanmu, mutanenmu, da wuraren ibadarmu.”

Ya kuma tabbatar da ci gaba da kiyaye amanar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yana mai cewa Buhari ya bar wa Najeriya tarihin nasara.

A nasa jawabin, gwamna Radda ya gode wa shugaban ƙasa kan goyon bayansa ga jihar, yayin da tsohon gwamna Aminu Masari da Wazirin Katsina, Ibrahim Ida, suka yaba da ayyukan ci gaba da Tinubu ke aiwatarwa a jihar, tare da neman ƙarin kulawa musamman a fannin tsaro da filin jirgin sama na Katsina.

Leave a Reply