Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a, a matsayin ranar hutun Mauludi
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 5 ga Satumba, 2025 a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
Wata sanarwa da babban sakatariyar ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Magdalene Ajani ta fitar a madadin ministar, ta taya al’ummar Musulmin Nijeriya da ma wajenta murna, inda ta bukaci yin tunani a kan kyawawan dabi’un Manzon Allah na zaman lafiya, soyayya, tawali’u, juriya, da tausayi.
KU KUMA KARANTA: Islamiyoyi sama da 700 ne suka halarci zagayen Maulidin Annabi Muhammad (SAWW) a Potiskum
Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya na dukkan addinai da su yi amfani da wannan damar wajen yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali, tare da marawa yunkurin gwamnati na hadin kai da ci gaba.
Ministan harkokin cikin gida yana yiwa al’ummar musulmi barka da Sallah lafiya.









