Tinubu ya mayar da shugaban NTA na ƙasa da aka sauke
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da tsohon shugaban hukumar Talbijin na Ƙasar, NTA da aka sauke kwanan nan, Salihu Abdullahi Dembos.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a 2023 – a yanzu zai dawo domin kammala wa’adin mulkinsa na shekara uku.
KU KUMA KARANTA: Tinubu ya naɗa Pedro a matsayin sabon shugaban gidan talabijin na ƙasa, NTA
A ƴan kwanakin nan ne aka sanar da sauke Dembos sakamakon wasu sauye-sauye da aka gudanar da hukumar.
Sauke shi ya janyo zazzafar muharawa da suka musamman daga yankin arewacin ƙasar, inda Salihu Abdullahi Dembos ya fito.
Haka ma shugaban ƙasar ya bayar da umarnin maido da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA, domin shi ma ya ƙara wa’adinsa na shekara uku da zai ƙare a 2027.









