NDLEA a Kano ta kama tabar wiwi da kwalaben Akurkura dubu 8
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta Jihar Kano ta kama kwalabe 8,000 na Akuskura da kuma bulo 48 na tabar wiwi, tare da cafke wani mutum mai shekara 37 da ake zargi.
Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, 2 ga Satumba, 2025, ta hannun kakakinta ASN Sadiq Muhammad Maigatari.
Sanarwar ta ce an cafke wanda ake zargin mai suna Ali Muhammad ne a kan titin Zariya zuwa Kano, kusa da gadar Tamburawa, bayan da jami’an NDLEA suka dakatar da wata motar tirela daga Legas wadda ke kan hanyar zuwa Maiduguri.
KU KUMA KARANTA: NDLEA ta kama dattijo mai shekaru 75, da Tabar Wiwi
An gano cewa an ɓoye kayan ne a tsakanin baburan Adaidaita Sahu da tirelar ta ɗauko, inda aka ƙera rufin katako a ƙasan tirelan domin ɓoye kayan.
Hukumar ta ce kayayyakin da wanda ake zargin na hannunta, kuma za a ci gaba da gudanar da bincike tare da yin gwaji a dakin gwaje-gwaje domin tantance sinadaran da ke cikinsu.