Unkuji Ƙwara ya gargaɗi matasan Azare masu ƙwacen waya, mashin da ɓalle shaguna

0
237
Unkuji Ƙwara ya gargaɗi matasan Azare masu ƙwacen waya, mashin da ɓalle shaguna

Unkuji Ƙwara ya gargaɗi matasan Azare masu ƙwacen waya, mashin da ɓalle shaguna

Daga idris Ibrahim Azare

Magajin Ali Ƙwara wanda ya ƙware wajen taimakawa ‘yansandan Najeriya wajen daƙile manyan ɓarayi ‘yan fashi da makami a sassan ƙasar nan don kawo zaman lafiyar al’umma.

A cewarsa ‘yan kwanakin nan ya samu kiraye-kiraye daga al’ummar garin Azare da ya kawo masu ɗauki sakamakon yadda yara matasa ɓatagari suke addabar su da ƙwacen waya da ɓalle shagunan da haura gidajen da sauran ire-iren waɗannan laifuka.

Unkuji ya ce yanzu zai sa kafar wando ɗaya da duk wani ƙaramin ɓarawo marar kunya.

Don haka wannan gargaɗi ne ga iyayen yara kan cewa in ya kama yaro, kar wani Uba ko ɗan uwan ɓarawo ya biyo sayu gidansa. Tun da iyaye sun gagara kula da ‘ya’yansu sun sa soyayya ga ‘ya’yansu ba sa faɗa musu gaskiya da ba su tarbiyar da Allah ya ɗora musu.

Unkuji ya ƙara da cewa, yanzu muna nan mun sa ƙasar a gaba muna gumurzu da manyan ɓarayi masu manyan bindiga a lungu da saƙo na ƙasar nan a wasu jihohi da suke addabar jama’a kuma ana samun nasarori wajen daƙilesu.

KU KUMA KARANTA: Ana fargabar ‘yan bindiga sun sake ɗiban ɗalibai a jami’ar tarayya ta Dutsinma

Ya bayyana cewa zai gyara cikin Azare ta yadda zai cafke masu sayar da tabar wiwi da ƙwayoyi da sauran ababen shaye-shaye da matasan ke sha yana gurɓatar da tunanin su suna aikata munanan laifuka. Don haka kowa ya shafawa kansa ruwa. Inji

A ƙarshe Unkuji ya yi kira ga tsagerun matasan da su jefar da makamansu su rungumin sana’a domin idan suka ci karo da shi abin da zai biyo baya ba zai yi daɗi ba.

Idan kuma rashin abin yi ne yake sa matasan aikata wannan, ya yi alƙawarin su kawo kansu zai tallafe su da ƙaramin jari don su zama na gari, subbar garin ya zauna lafiya.

Garin na Azare dai ya faɗa cikin wani yanayi da wasu matasa suke ƙwacen wayoyi da mashinan hawa tare da haura gidajan mutane suna ƙwatar duk abin da suka ci karo da shi.

Leave a Reply