Babban Malami, Sheikh Mukhtar Arzai Kano ya rasu
Daga Jameel Lawan Yakasai
Allah ya yi wa babban malamin musulunci, Khalifan Sheikh Manzo Arzau Khalifa Muktar (Alaramma) Sheikh Manzo Arzai, a Kano.
Shehin malami Imam Muhammad Nur Muhammad Arzai ne ya sanar da rasuwar.
Ya ce za a gudanar da jana’izarsa ranar Lahadi da misalin ƙarfe 2:30 na rana, a Zawiyar Sheikh Manzo Arzai, da ke Unguwar Arzai a Kano.
KU KUMA KARANTA: Gamayyar gwamnonin arewa sun yi alhinin rasuwar Sheikh Sa’eed Hassan Jingir
Marigayin ya shafe rayuwarsa cikin alʼamuran hidindinmun addinin musulunci.
Al’ummar musulmi na ci gaba da bayyana ta’aziyyarsu tare da addu’ar Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa, Ya kuma haɗa shi da Manzon Allah (SAW).









