Muna fuskatar matsin lamba – Shugaban NNPC

0
130
Muna fuskatar matsin lamba - Shugaban NNPC
Shugaban NNPC Ojulari

Muna fuskatar matsin lamba – Shugaban NNPC

Daga Jameel Lawan Yakasai

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC Ltd.), Eng. Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana cewa kamfanin na fuskantar matsin lamba daga waɗanda ba su son ci gaban ƙasa da kuma sauye-sauyen da ake aiwatarwa a NNPC.

Shugaban na wannan furuci ne yayin da yake karɓar tawagar ƙungiyar ma’aikatan man fetur (PENGASSAN) a hedkwatar kamfanin da ke Abuja a ranar Alhamis.

Ya ce duk da matsin lamba, shugabancin kamfanin ba zai kasa a gwiwa ba, domin sauyi yakan zo da tsada amma manufar ita ce amfanin al’umma baki ɗaya.

Ojulari ya jaddada cewa dole ‘yan Najeriya suka kara hakuri domin samun nasarar sauye-sauyen da za su kawo alfanu ga ƙasa da al’ummarta.

Ya kuma bayyana cewa tun bayan hawansa kan shugabanacin kamfanin kusan watanni biyar da suka gabata.

KU KUMA KARANTA: Ribar da muke samu ta ragu da kashi 79% a watan Yuli – NNPC

Shugabancin kamfanin ya maida hankali wajen farfaɗo da matatun mai ta hanyar haɗin gwiwa da bangarori daban daban domin tabbatar da dorewa da da kuma samun riba. “Ba za mu yi aiki cikin gaggawa domin biyewa masu matsin lamba kawai ba. Muna son tabbatar da cewa matatun za su yi aiki yadda ya kamata na dogon lokaci,” a cewar sa.

A nasa jawabin, shugaban PENGASSAN, Comrade Festus Osifo, ya gode wa NNPC bisa haɗin gwiwar da suka basu yayin taron Energy & Labour Summit 2025 da aka gudanar a Abuja,

Tare da yabawa nasarorin da aka samu a ƙarƙashin shugabancin Ojulari. Ya ce an samu raguwar satar man fetur da kuma ƙaruwar samar da danyen mai, tare da tabbatar da cewa “PENGASSAN za ta ci gaba da mara wa NNPC baya don dorewar tsarin domin amfanin Najeriya baki ɗaya.”

Leave a Reply