Islamiyoyi sama da 700 ne suka halarci zagayen Maulidin Annabi Muhammad (SAWW) a Potiskum

0
173
Islamiyoyi sama da 700 ne suka halarci zagayen Maulidin Annabi Muhammad (SAWW) a Potiskum
Dandazon al'ummar musulmi a wajen taron Maulidi a Potiskum

Islamiyoyi sama da 700 ne suka halarci zagayen Maulidin Annabi Muhammad (SAWW) a Potiskum

A safiyar yau Asabar ɗaruruwan al’ummar musulmi masoya Manzon Allah (S) maza da mata, tare da makarantun Islamiyoyi sama da 700 ne suka halarci taron zagayen Maulidin Annabi Muhammad (SAWW) kamar yadda suka saba a kowace Asabar ɗin farko na watan Rabi’ul Auwal.

Dandazon al’ummar sun taru ne a fadar mai martaba Sarkin Fika da ke Potiskum, inda aka hau sahu ana tafiya, ana rera waƙoƙin yabon Annabi (S), kowa ka gani cikin farin ciki da annashuwa.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Iran ta yi afuwa ga fursunoni 1,000 albarkacin ranar Maulidi

Zagayen Maulidin ya bi kusan dukkan manyan titunan cikin garin Potiskum. Inda a ƙarshe, Malamai daga kowane ɓangare na al’ummar suka gabatar da jawabi a ƙofar fadar Sarkin Fika ɗin.

Leave a Reply