Gwamnatin tarayya ta bawa Nafisah Abdullahi, wacce ta lashe gasar Turanci ta duniya kyautar Naira dubu 200

0
210

A yau Alhamis, Gwamnatin Tarayya ta baiwa Nafisah Abdullahi, wadda ta lashe gasar TeenEagle Global Finals, kyautar N200,000.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya mika wannan lambar yabo a wani biki da aka gudanar a Abuja.

A baya-bayan nan, Atiku Foundation ta baiwa zakarun gasar TeenEagle — Nafisa Abdullahi, Rukaiya Fema da Khadija Kalli — guraben karatu da aka dauki nauyinsu saboda bajintar da suka nuna a gasar TeenEagle Global Finals.

KU KUMA KARANTA: ‘Yar jihar Yobe ta lashe gasar Turanci ta Duniya a Burtaniya

Wadannan ‘yan mata, wadanda suka fito a matsayin zakarun duniya a fannoni daban-daban na gasar, sun samu yabo daga gudauniyar saboda abin da ta kira “nasara mai ban mamaki.”

Daga cikin wadanda suka samu wannan yabo akwai Nafisa Abdullahi ‘yar shekara 17, wadda ta fito fili saboda kwarewarta a harshen Ingilishi, tunani mai zurfi da kuma iya bayyana magana, abubuwan da suka taimaka mata wajen doke mahalarta daga kasashe 69.

Leave a Reply