Kotu a Kano ta ba da umarnin a binciki ɗan jarida Jaafar Jaafar bisa zargin ɓata suna

0
251
Kotu a Kano ta ba da umarnin a binciki ɗan jarida Jaafar Jaafar bisa zargin ɓata suna
Ɗan jarida Jaafar Jaafar

Kotu a Kano ta ba da umarnin a binciki ɗan jarida Jaafar Jaafar bisa zargin ɓata suna

Daga Jameel Lawan Yakasai

Wata kotu a Kano ta bayar da umarnin umurtar mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya da ya gudanar da cikakken bincike kan laifukan da ake zargin Jafar Jafar mawallafin jaridar Daily Nigerian da ke Kano.

Shari’ar da aka gabatar a gaban babban kotun majistare mai lamba 15, karkashin jagorancin Malam Abdul’aziz M. Habib, daraktan kula da jama’a na gidan gwamnatin Kano, Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo ne ya shigar da ita, wanda ya kai mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jafar Jafar, da wani Audu Umar a gaban kotun majistare ta Kano bisa zargin bata masa suna ta hanyar bayyana shi a matsayin “barawon hadimi” ga gwamnan jihar Kano.

A karar da aka shigar karkashin sashe na 106 da 107 na dokar hukumar shari’a ta jihar Kano 2019, da sashe na 114, 164, da 393 na kundin laifuffuka na jihar Kano, DG Protocol na neman gurfanar da wadanda ake kara biyu.

KU KUMA KARANTA: Barau Jibrin ya fi Ganduje hannu a haddasa rikicin siyasar Kano – Jaafar Jaafar

Takardar wadda aka shigar a ranar 28 ga watan Agusta 2025 a gaban Alkalin Kotun Mai shari’a Abdulazeez M. Habib na Kotun 15 da ke Nomansland, Kano, ta zargi Jafar da Umar da bata masa suna a idon jama’a da kalaman karya da ke cutar da mutuncin sa da kuma shugaban sa Gwamna Abba Kabir Yusuf.

A halin da ake ciki, babban alkalin kotun majistare na 15, Nomansland, ya umurci mataimakin babban sufeton ‘yan sanda na shiyyar ta daya, Kano, da ya kaddamar da cikakken bincike kan zargin bata suna da ke kunshe cikin rahotannin da Daily Nigerian ta wallafa.

A baya dai gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da batun cire kudi da kuma karkatar da kudaden jihar da suka kai Naira biliyan 6.5 zuwa asusun daidaikun mutane.

Leave a Reply