BBC Hausa ta ƙi amince wa da takardar murabus ɗin shugaban sashin Hausa Aliyu Tanko
Daga Jameel Lawan Yakasai
Kafar yaɗa labaran BBC ta dakatar da Editan ta na sashen Hausa, Aliyu Tanko, na tsawon watanni uku bisa zarginsa da cin zarafin wata tsohuwar ma’aikaciyar gidan, maisuna Halima Umar Saleh.
BBC ta kafa kwamitin bincike kan ƙorafe-ƙorafe daban-daban da wasu tsoffin ma’aikata har da na yanzu sashen Hausa da suka shigar a kansa kamar yadda Iconic Fm ta ruwaito.
Wata majiya mai tushe ta ce mataimakin babban jami’in gudanarwa na BBC News, kuma Daraktan BBC News Global, Jonathan Munro, shi ne ya bada umarnin gudanar da binciken, inda ya turo tawaga daga kasar Landan zuwa Kasar Najeriya Abuja domin gudanar da shi.
KU KUMA KARANTA: Ma’aikatan BBC sun yi zanga-zanga kan dakatar da abokin aikinsu
Har ilayau wata majiya ta shaida cewa an dakatar da Tanko ne a ranar Laraba, amma abin mamaki ya miƙa takardar yin murabus a ranar Alhamis, lamarin da aka ƙi amincewa da shi.
Majiyar ta ƙara da cewa an shaida masa cewa ba zai yiwu ya yi murabus ba a halin yana ƙarƙashin dakatarwa da kuma bincike.









