Mun karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776, mun warware rikicin aure 621 a shekarar 2024 – Hukumar Hisbah ta Kano 

0
201
Mun karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776, mun warware rikicin aure 621 a shekarar 2024 - Hukumar Hisbah ta Kano 

Mun karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776, mun warware rikicin aure 621 a shekarar 2024 – Hukumar Hisbah ta Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a shekarar 2024, ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776, tare da warware rikicin aure 621.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da Kwamandan Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya aikowa da Jaridar Neptune Prime.

Inda yace hukumar ta hisbah ta fasa dubban kwalaben giya wanda kotu ta bayar da umarni.

Haka kuma ta karɓi sabbabin waɗanda suka karɓi musulunci.

Sannan kuma hukumar ta tara kuma ta raba kuɗaɗen tallafi mai yawa kuma ta karɓo bashi da kudin shawarwa, aka gaza biya da ya kai Naira miliyan 212,334,839.

Kwamandan rundunar, Sheikh Amin Ibrahim Daurawa, ya ce tun bayan zuwan Gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar 29 ga Mayu, 2023, an inganta harkokin Hisbah domin ciyar da ayyukanta gaba.

KU KUMA KARANTA: Hisbah za ta aurar da tubabbun ‘yan daba a Kano

Ayyukan da hukumar ta gudanar sun haɗa da:

Auren Gata ga ma’aurata 3,800.

Horon ƙwarewa ga jami’an Hisbah 1,000.

Rabon kayan tallafi ga marayu, gwauraye da gajiyayyu.

Taimakawa wajen aikin Hajji daga Kano zuwa Saudiyya.

A halin yanzu, rundunar tana da fiye da jami’ai 12,436,00. da ke aiki a kananan hukumomi 44 na jihar, tare da sassan ayyuka da dama ciki har da bangaren mata karkashin jagorancin Dr. Khadija Sagir Suleiman.

yawan yan Hisbah mata(2362.)

Gwamnatin Kano ta bayyana shirin kafa :

1. Makarantar horar da jami’an rundunar,

2. ƙara albashi da tsarin ritaya ga jami’an Hisbah,

3. Sabbin kayan aiki.

4. Gina sabuwar hedikwatar hukumar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa Hisbah don tabbatar da adalci, zaman lafiya da ɗorewar ɗabi’u masu kyau a Kano.

Leave a Reply