NDLEA ta kama waɗanda ake zargi da sanya wa masu zuwa ƙasar Saudiyya ƙwayoyi a cikin kayansu
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce ta kama wani Mohammed Ali Abubakar da aka fi sani da Bello Karama da ake zargin babban mai safarar ƙwayoyi ne tare da wasu mutane biyar masu aiki a airport da ake zargi da yi wa mahajjata cushen ƙwayoyi a cikin kayansu a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA).
Cikin wata sanarwar da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar bayan taron manema labarai a shalkwatar NDLEA ta ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin, 25 ga Agusta, 2025.
Sanarwar ta bayyana cewa binciken NDLEA ya gano cewa mutanen sun shirya lodin jakunkuna shida a jirgin Ethiopian Airline daga Kano zuwa Jeddah, a ranar 6 ga Agusta, 2025.
Uku daga cikin jakunkunan na ɗauke da ƙwayoyi, wadanda abin ya rutsa da su su ne Maryam Hussain Abdullahi, Abdullahi Bahijja Aminu da Abdulhamid Saddiq, waɗanda suka je aikin Umrah.
KU KUMA KARANTA: NDLEA ta kama matashi ɗauke da ƙwayoyin Tramadol 7,000 a Kano
Sanarwar ta ce sun isa Saudiyya ne ba tare da sanin cewa an saka wa waɗannan jakunkuna da ƙwayoyi ba, abin da ya jawo aka tsare su a Jeddah.
NDLEA ta ce an gano Bello Karama shi ne ya kawo jakunkunan, inda daga baya ya bi jirgin Egypt Air zuwa Jeddah, yayin da ya bar jakunkunan da aka saka musu sunayen waɗannan matafiyan a Ethiopian Airline.
Babafemi ya ce an riga an kama mutane shida cikin waɗanda ake zargi da hannu, kuma sun amsa laifinsu.









