Ƙungiyar limaman Juma’a a Jigawa, ta raba littattafan da za ana karantawa a huɗubobin juma’a

0
244
Ƙungiyar limaman Juma'a a Jigawa, ta raba littattafan da za ana karantawa a huɗubobin juma'a

Ƙungiyar limaman Juma’a a Jigawa, ta raba littattafan da za ana karantawa a huɗubobin juma’a

Daga Jameel Lawan Yakasai

Kungiyar Limaman Masallatan Juma’a ta kasa reshen Jigawa ta ce ta raba littattafan hudubar Juma’a ga limamai domin gabatarwa a masallatai.

Ya ce an raba littattafan ne ga limaman masallatai 1,664 domin ba su damar zabar huɗubobi da za su rika gabatarwa a ranakun Juma’a.

Malam Galamawa ya bayyana cewa za a shirya taron bita ga limaman domin wayar da kai kan manufar littafin, fa’idarsa da kuma wasu kalmomin da aka yi amfani da su.

KU KUMA KARANTA: NLC Kaduna Ta Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman A Masallacin Juma’a Na SMC

Ya ƙara da cewa limamai suna da rawar gani wajen yi wa addinin Musulunci hidima ta hanyar wa’azi, ilmantarwa da kuma gyaran tarbiyya a zukatan al’umma.

Sakataren ƙungiyar ya kuma bukaci a ci gaba da mutunta limamai saboda daraja da ɗaukaka da Allah ya yi musu.

Leave a Reply