NDLEA a Kano ta cafke matashi da tabar wiwi ta sama da Naira Miliyan 10
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), reshen jihar Kano, ta ce ta kama wani matashi mai shekaru 27, Umar Adamu-Umar, da tabar wiwi nauyin kilo 9 da darajarta ta haura Naira miliyan 10.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar a Kano, Malam Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar a ranar Asabar.
Ya bayyana cewa jami’an NDLEA da ke karkashin ofishin Kiru sun cafke wanda ake zargi, mazaunin ƙaramar hukumar Fagge ta Kano, a ranar 6 ga watan Agusta a kan titin Zaria – Kano, lokacin da yake jigilar buhunan wiwi guda 19 daga Legas zuwa Kano.
KU KUMA KARANTA: NDLEA ta kama maniyyata a filin jirgin saman Kano, bisa zargin safarar hodar Iblis zuwa ƙasar Saudiyya
“Wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin harkar safarar miyagun ƙwayoyi, kuma an dade ana sa ido a kansa,” in ji Muhammad-Maigatari.
“Cire wannan adadi daga hannun masu safara zai kuma kare al’umma daga illolin zamantakewa da tattalin arziki da ke tattare da kasuwancin miyagun ƙwayoyi,” in ji shi.
Kakakin hukumar ya ce sashen dabarun NDLEA a ƙarƙashin jagorancin Abubakar Idris-Ahmad zai ƙara tsaurara sintiri da kuma amfani da bayanan leƙen asiri domin dakile safarar miyagun ƙwayoyi a jihar Kano.









